Rabiba Aboubacar Bouzou: Kasar Sin dake karkashin jagorancin jam’iyyar kwaminis abun koyi ne ga kasashe masu tasowa
2022-10-18 15:01:17 CMG Hausa
Ana ci gaba da gudanar da babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20 a halin yanzu a Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ko kuma JKS a takaice, mai tarihin shekaru 101, ta shafe tsawon shekaru 73 tana kan karagar mulkin kasar, wato tun kafuwar Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin. Babban taron wakilan jam’iyyar, gami da kwamitin kolinta, su ne hukumar koli ta jam’iyyar. A kan gudanar da babban taron wakilan jam’iyyar a duk bayan shekaru biyar.
A lokacin bikin kaddamar da taron a ranar Lahadi 16 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wani muhimmin jawabi, inda ya waiwayi wasu manyan nasarori na ban mamaki da suka wakana a kasar Sin cikin shekaru 5 da suka gabata, tun bayan babban taron wakilan JKS karo na 19 da ya gabata.
Ya ce kwamitin kolin JKS ya yi aiki tukuru, wajen cimma nasarorin farfado da kasa, a gabar da duniya ke fuskantar manyan kalubale, irin wadanda ba a ga kamar su ba cikin wannan karni. Ya ce kwamitin koli ya yi rawar gani, wajen tsara managartan manufofin raya jam’iyya da ma kasa baki daya.
Game da wannan muhimmin taro, Murtala Zhang ya samu damar zantawa da Hajiya Rabiba Aboubacar Bouzou, shugabar Jaridar Sahel dake Jamhuriyar Nijar, wadda ta taba zuwa kasar Sin don karo ilimi daga shekara ta 2012 zuwa ta 2013. Rabiba Bouzou ta bayyana ci gaban da kasar Sin ta samu a idonta, da yin fashin baki kan muhimmiyar rawar da jam’iyyar kwaminis mai mulkin kasar Sin ke takawa.
Jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ta ayyana wasu muhimman burika biyu wajen samar da ci gaban kasar. An riga an cimma buri na farko, wato zuwa shekara ta 2021, lokacin cika shekaru 100 da kafuwar jam’iyyar kwaminis ta kasar, inda aka gina al’ummar kasar Sin mai matsakaiciyar wadata daga dukkan fannoni. Kana, wannan rahoton da shugaba Xi ya gabatar a ranar Lahadi, ya yi hangen nesa, da tsara muhimman ayyukan da za’a gudanar, domin neman cimma buri na biyu, wato zuwa shekara ta 2049, lokacin cika shekaru 100 da kafa Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin, inda za’a gina kasar Sin dake bin tsarin gurguzu na zamani, da wadata daga dukkanin fannoni.
Rahoton ya kuma ce, kasar Sin ta kama sabuwar hanyar zamanantar da kanta daga dukkan fannoni, kana, shekaru biyar masu zuwa, lokaci ne mafi muhimmanci. Rahoton ya bullo da wasu sabbin dabaru, da tsare-tsare, gami da matakai na neman cimma babban buri na biyu a fannoni da dama, ciki har da samar da ci gaba mai inganci, da inganta horas da kwararru, da tabbatar da jigon al’umma, da inganta rayuwar al’umma, da shimfida zaman jituwa tsakanin dan Adam da muhalli, da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali, da makamantansu.
Hajiya Rabiba Bouzou ita ma ta yi hangen nesa kan makomar hadin-gwiwar kasarta Nijar da kasar Sin.
Wakilan jam’iyyar, gami da wadanda aka ba su goron gayyata na musamman sama da 2300 sun halarci taron, tare da wasu da ba ’yan jam’iyyar kwaminis din ba da sauransu. Za kuma a rufe taron a ranar 22 ga wata.
A wajen taron, za’a amince da gyararren shiri na kundin ka’idojin jam’iyyar JKS, da kuma zabar membobin kwamitin kolin jam’iyyar da na kwamitin ladabtarwar jam’iyyar a sabon zagaye. (Murtala Zhang)