logo

HAUSA

Ma'aikatar Harkokin Wajen Sin: Shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” ta haifar da sabon salo na hadin gwiwar kasa da kasa

2022-10-18 21:00:36 CMG Hausa

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" ta zarce tsohon tunanin kasa da kasa, na neman moriya bisa bambancin labarin kasa, tare da samar da wani sabon salo na hadin gwiwar kasa da kasa.

Wang ya bayyana haka ne a yayin taron manema labaru da aka saba yi a yau Talata.

An ce, nan da shekaru tara bayan gabatar da shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya", ta haifar da babban tasiri a duniya. A sa'i daya kuma, ana tsokaci da cewa, kasar Sin na inganta shawarar domin cimma moriyarta a fannin siyasa. Game da wannan batun, Wang ya jaddada cewa, shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya " ba rufaffiyar da'ira ba ce, maimakon haka babban dandamali ne budadde kuma mai hade da bangarori daban daban. Kana shawarar ba kasar Sin ce ke “yin kidanta ta yi rawar ta ita kadai ba”, maimakon haka “rawa ce da take takawa” tare da sauran abokai.

A cewarsa, kasar Sin a bude take ga duk bangarorin da suka shiga ayyukan raya shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya", kuma a shirye take don yin la'akari, da hade shawarar raya manyan ababen more rayuwa da wasu kasashe suka gabatar, don samar da duniya da kayan aikin jama'a masu inganci.

Yayin da yake ba da amsa kan muhimmancin ra’ayin gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adam kan duniyar dake halin yanzu, Wang ya bayyana cewa, a duniyar yau dake fama da yaduwar annobar COVID-19, tabarbarewar tattalin arziki, da rikice-rikice da yake-yake, ra’ayin gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adam, amsa ce mai karfi ga raba gari ta fannin tattalin arziki, da kafa “kananan kungiyoyi” bisa bambancin ra’ayi da dai sauransu. Yana da matukar muhimmanci, kuma ya zama tuta mai haskakawa dake jagorantar zamanin yau. (Mai fassara: Bilkisu Xin)