logo

HAUSA

Shugaba Xi ya jagoranci taro na 2 na rukunin shugabancin babban taron JKS na 20

2022-10-18 21:32:44 CMG Hausa

Da yammacin yau Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jagoranci taro na 2 na rukunin shugabancin babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin(JKS) na 20.

Taron na yau ya amince da mika daftarin kudurori kan rahoton kwamitin koli na JKS na 19, da rahoton aiki na kwamitin ladabtarwa na kwamitin kolin, da gyaran fuska ga kundin ka’idojin JKS, domin wakilan jam’iyyar su duba tare da tattaunawa a kai.

Kaza lika, taron ya amince da jerin sunayen da aka gabatar domin neman nada su mambobi da mambobin karba karba na kwamitin kolin JKS na 20, da ma mambobin kwamitin ladabtarwa. An kuma amince da mika jerin sunayen ga taron wakilan jam’iyyar domin tattaunawa a kai.  (Saminu Alhassan)