logo

HAUSA

Kasar Sin ce babbar misali na yadda ya kamata demokradiyya ta kasance

2022-10-18 18:46:19 CMG Hausa

Demokradiyya ita ce tsarin shugabanci dake mayar da hankali kan muradun al’umma. Wato dai, al’umma ne ya kamata su kasance kashin bayan demokradiyya. Kuma kasar Sin ce babbar misali na yadda ya kamata demokradiyya ta kasance, domin a ganina, tabbatuwar tsarin demokradiyya ita ce, kasancewar al’umma cikin walwala da wadata da kwanciyar hankali.

Yayin da yake kaddamar da babban taron wakilan Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin karo na 20 a Lahadin da ya gabata, shugaban kasar Xi Jinping, ya jaddada cewa kasar za ta kara inganta tsarin demokradiyyar dake mayar da hankali kan jama’a, wato jama’a ne za su kasance masu ruwa da tsaki a dukkan tsarukan demokradiyya a dukkan matakai.

Abun da na fahimta shi ne, a ko da yaushe, JKS ta kan tsara manufofi da dabarun da za su tabbatar da cewa, al’umma ne ke kan gaba a duk wani abun da ya shafi kasar, wanda ke nuna yadda take mayar da hankali wajen lalubo dabarun da suka dace da yanayin da take ciki domin amfanawa al’ummarta.

Karkashin shugabancin JKS cikin shekaru 100 da suka gabata, kowa zai iya shaida cewa, kasar Sin ta samu manyan nasarori na ban mamaki da babu wata kasa da ta samu a duniya. Misali na baya-bayan nan shi ne, fatattakar talauci baki daya. Duk da yawan al’ummarta da kuma kasancewarta kasa mai tasowa, Sin ta yi abun da manyan kasashe suka gaza. Ta tabbatar da dukkan al’umominta daga kabilu daban daban na cikin wadata ba tare da barin kowa a baya. Haka kuma, ta tabbatar da cewa ana rayuwa cikin kwanciyar hankali da lumana a tsakaninsu.

Jama’a su suka san matsalolinsu, kuma damawa da su cikin harkokin kasa, shi zai kai ga ci gaban da ake muradi. Wakilan jam’iyyar daga dukkan bangarori, da suka hada da manoma da ma’aikata daga bangarori daban-daban na samun damar wakiltar al’ummominsu yayin taron wakilan jam’iyyar Kwaminis ta kasar, lamarin dake kara jaddada cewa, al’umma ne ke jan ragamar demokradiyyar kasar, kuma wannan tsari ne ya kai ta ga samun dimbin nasarori. (Fa’iza Mustapha)