logo

HAUSA

Dabarar da kasar Sin ta dauka wajen zamanintar da al'umma

2022-10-18 09:59:03 CMG Hausa

A ranar Lahadin da ta gabata, aka kaddamar da babban taron wakilan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS) karo na 20 a birnin Beijing na kasar, inda Xi Jinping, babban sakataren jam'iyyar, ya gabatar da wani rahoto.

Cikin rahotonsa, Xi ya jaddada cewa, dabarar zamanintar da al'umma da kasar Sin da dauka, ana aiwatar da ita ne karkashin jagorancin JKS, tare da bin tsarin siyasa na Gurguzu. Wasu halayen musamman da dabarar ke da su, sun hada da yadda ake dora muhimmanci kan moriyar jama’a, da kokarin samun daidaito tsakanin dan Adam da muhalli, gami da neman kulla huldar hadin kai da ke iya amfanar dukkan bangarori masu ruwa da tsaki.

Ban da haka, dabarar zamanintar da al’ummar Sin ta kunshi wasu ginshikai, da suka hada da nacewa ga zama karkashin jagorancin JKS, da tsarin Gurguzu mai halin musamman na kasar Sin, da neman samun ci gaba mai inganci, da aiwatar da dukkan ayyukan gwamnati bisa tafarkin demokuradiyya, da baiwa dukkan al'ummar kasar damar samun wadata tare, da kafa al'ummar dan Adam mai kyakkyawar makoma ta bai daya a duniya, da kirkiro sabon nau'in wayewar kai ta bil Adama, da dai sauransu. Wannan bayanin da aka gabatar ya nuna hanyoyin da za a bi don raya kasar Sin zuwa wata kasar zamani mai bin tsarin Gurguzu. (Bello Wang)