logo

HAUSA

Ya kamata jama’ar kasar Sin su yi kokari tare don sa kaimi ga farfadowar al’ummar kasar Sin

2022-10-17 14:39:21 CMG HAUSA

 

A yayin da shugaba Xi Jinping yake halartar taron tattaunawa na tawagar wakilan jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin daga yankin Guangxi yau da safe, ya jaddada cewa, an tsara taswirar raya sha’anin jam’iyyar da kasar a gun taron wakilan JKS karo na 20, kuma taron ya ba da sanarwar siyasa da shirin gudanar da harkokin kasa bisa jagorancin jam’iyyar Kwaminis ta Sin, kana jama’ar kasar daga kabilu daban daban, za su ci gaba da kokarin raya tsarin gurguzu mai halin musamman na kasar Sin.

Idan har ana son kara fahimtar manufar taron wakilan JKS karo na 20, wabiji ne a fahimci ayyukan da aka gudanar a shekaru 5 da suka gabata, da babbar ma’anar kwaskwarimar da aka yi a cikin shekaru 10 da suka gabata a sabon zamani, da muhimman ayyukan farfado da al’ummar kasar Sin ta hanyar zamanintar da kasar mai alamar kasar Sin, da martaba bukatun raya al’umma ta hanyar yin kwaskwarima, da kuma yin hadin gwiwa da hada kai tare. Ya kamata dukkan membobin JKS da daukacin jama’ar kasar Sin daga kalibu daban daban, su hada karfi da karfe, da yin kokari tare don sa kaimi ga raya al’ummar kasar Sin. (Zainab)