logo

HAUSA

Kasar Sin ta taimakawa mutane dubu 100 dake kauyuka a Uganda damar kallon shirye-shirye ta tauraron dan-Adam

2022-10-17 10:48:42 CMG HAUSA

 

A ranar Asabar din da ta gabata ce, kasar Sin ta yi nasarar kammala aikin kafa na’urar kama shirye-shiryen talabijin ta tauraron dan-adam a kauyuka 900 dake kasar Uganda a hukumance, wadanda a baya suke fuskantar kalubalen hanyoyin sadarwa.

Ministan watsa labarai, sadarwa da fasaha da ba jagoranci na kasar Uganda Chris Baryomunsi ne, ya jagoranci bikin mika aikin da aka gudanar a kauyen Katabi dake gundumar Wakiso a tsakiyar kasar.

Ya yabawa kasar Sin bisa tallafin fasaha da take baiwa Uganda. Yana mai cewa, tallafin zai taimaka wajen samar da ci gaba ga al’ummomin yankin.

A nasa bangare, babban jami’in gudanarwa na kamfanin StarTimes dake kasar Uganda Aoge Mengdai, wanda kuma ke kula da aikin, ya bayyana cewa, tun daga shekarar 2018 da aka fara aiwatar da aikin zuwa yanzu, an hada kauyuka 900 da hidimar kama shirye-shiryen talabijin ta tauraron dan-Adam, baya ga fiye da mutane dubu 100 a gidajen iyalai dubu 18 da makarantu dubu 2 da 700, da cibiyoyin kiwon lafiya dake iya kallon shirye-shiryen talabijin ta tauraron dan-Adam.

Mengdai ya bayyana cewa, amfanin hidimar kama shirye-shiryen talabijin din, ya zarce shiga talabijin kawai. Yana mai cewa, a halin yanzu yaran dake wadannan kauyuka, suna iya samun damar koyo ta talabijin da kallon abubuwa ta hotunan bidiyo, wanda ke da matukar amfani a harkar ilimantarwa a zahiri. Bugu da kari, za su iya gogayya da sauran makarantu dake wajen al’ummarsu.

Kamfanin StarTimes, kamfani ne na kasar Sin dake samar da hidimar kama shirye-shiryen talabijin ta hanyar biyan kudi. (Ibrahim Yaya)