logo

HAUSA

Hukumar UNOCHA ta yi gargadi game da barkewar cutar kwalara a kudancin Habasha

2022-10-17 10:42:15 CMG HAUSA

 

Hukumar kula da agajin jin kai ta MDD, ta yi gargadi game da yaduwar cutar kwalara a kudancin Habasha, yayin da ake samu karuwar masu kamuwa da ita.

Cikin sabon rahoton da ta fitar a ranar Alhamis, hukumar ta ce zuwa ranar 10 ga watan Oktoba, an samu mutane 191 da suka kamu da cutar a gundumomi 3 na yankin Bale, wadanda suka hada da Harana Buluk da Berbere da Delo Mena.

Kuma a wannan lokaci, an samu mace-mace 4 dake da alaka da cutar, inda jimilar adadin wadanda cutar ta yi ajalinsu ya kai kaso 2.09 cikin dari.

An samu mutum na farko da ya kamu da cutar ne a gundumar Harana Buluk a ranar 27 ga watan Augusta. A kuma ranar 18 ga watan Satumba, gundumar Berbere ta zamo wuri na biyu da aka samu bullar cutar, sai kuma gundumar Delo Mena inda aka samu rahoton a ranar 3 ga watan Oktoba.

A cewar hukumar, akwai yuwuwar amfani da ruwa mara tsafta daga gurbatattun cibiyoyin ruwa ne ya yi sanadin barkewar cutar. (Fa’iza Mustapha)