logo

HAUSA

Ta yaya cutar kyandar biri ta yadu tsakanin mutane?

2022-10-17 08:22:46 CMG Hausa

 

Cikin shirin da ya gabata, na yi karin bayani kan mene ne cutar kyandar biri wato Monkeypox a Turance, wadda ita ce wani nau’in cuta da ke yaduwa daga dabbobi zuwa mutane, kuma ta yi kama da dangin cutar agana wato Smallpox a Turance, wadda ta taba daukar dubban shekaru tana sanadin mutuwar mutane masu dimbin yawa a tarihin bil Adama.

Yau bari in yi muku bayani kan yadda cutar ta kyandar biri ke yaduwa daga dabbobi zuwa mutane.

Taba jinin dabbobin da suka kamu da cutar kyandar biri, da ruwan da ke cikin jikinsu, da fatarsu ko wuraren da suka jikkata kai tsaye, na iya haifar da yaduwar kwayar cutar kyandar biri daga namun daji zuwa bil Adama. Baya ga haka kuma, cin dabbobin da suka kamu da cutar, kuma ba a dafa su yadda ya kamata ba, yana kawo barazanar yaduwar cutar daga dabbobi zuwa ‘yan Adam. Galibi dai, ba safai kwayar cutar kyandar biri ta kan yadu tsakanin mutane ba. Taba abubuwan da suke fitowa daga sassan jiki masu taimakawa numfashi, da fatar da aka ji rauni, da kuma abubuwan da ke dauke da kwayar cutar, suna haifar da yaduwar cutar a tsakanin mutane. Idan mutane suna mu’amala da juna fuska da fuska, to, za a bukaci dogon lokaci kafin cutar ta yadu tsakanin mutane. Ban da haka kuma, mai yiwuwa kwayar cutar ta kyandar biri za ta yadu daga iyaye mata da jariransu sabbin haihuwa ta hanyar uwar cibiya ko kuma a lokacin haihuwa.

Hukumar kiwon lafiya ta kasa da kasa wato WHO ta jaddada cewa, domin rage barazanar kamuwa da cutar, ya kamata a kauracewa taba namun daji a wuraren da aka samu barkewar cutar kyandar biri, musamman ma taba mutanen da suka kamu da cutar ko kuma naman dabbobin da suka mutu sakamakon cutar ko jininsu ko sassan jikinsu ba tare da kariya ba. Sa’an nan kuma, ya zama tilas a dafa naman dabbobin sosai.

Hukumar WHO ta yi karin bayani da cewa, alamun kamuwa da cutar kyandar biri sun yi kama da na agana, amma ba su da tsanani sosai. A kan dauki kwanaki 6 zuwa 13 har ma 21 kafin alamun kamuwa da cutar kyandar biri sun bayyana. Da farko, wadanda suka kamu da cutar kan yi zazzabi, ciwon kai, kumburin kaluluwa, ciwon jijiyoyi, matukar gajiya da dai sauransu. Kumburin kaluluwa yana taimakawa wajen bambanta masu kamuwa da cutar kyandar biri da kuma masu kamuwa da cutar agana. Bayan kwanaki da dama, kuraje za su bayyana a fuska da sauran sassan jikin mutum, watakila kuma masu kamuwa da cutar za su kamu da ciwon huhu da dai sauransu.

Cutar kyandar biri, wani nau’in cuta ce da mutane sukan iya warkewa sakamakon kyautatuwar jikinsu. Yawancin masu kamuwa da cutar kan warke cikin makonni da dama. Nazari mai ruwa da tsaki ya nuna cewa, yin allurar rigakafin cutar kyandar biri yana kare mutane daga kamuwa da cutar har da kaso 85. (Tasallah Yuan)