logo

HAUSA

Neman kawo wa jama’a alheri shi ne burin JKS

2022-10-17 10:52:50 CMG HAUSA

 

A jiya ne, aka bude taron wakilan jam’iyyar Kwaminis ta Sin karo na 20 a birnin Beijing, inda babban sakatarem jam’iyyar Xi Jinping ya gabatar da rahoto. A cikin rahoton, an sha ambaton kalmar jama’a.

Idan aka waiwaiyi nasarorin da aka cimma wajen kyautata zaman rayuwar jama’a a cikin shekaru 10 da suka gabata, ko kuma tsara taswirar shirin neman zaman jin dadin jama’a a nan gaba, za a shaida burin jam’iyyar Kwaminis ta Sin na ganin jama’a sun yi rayuwa mai dadi da kuma farfadowar al’ummar kasar Sin, tare da tunanin shugaban kasar Sin na la’akari da muhimmancin jama’ar matuka. Wannan ya kara nunawa duniya dalilin da ya sa jam’iyyar Kwaminis ta Sin ta samu nasarar gudanar da ayyuka da dama.

Bisa shirin da aka tsara, kasar Sin za ta cimma burin zamanintar da kanta bisa tsarin gurguzu tun daga shekarar 2020 zuwa 2035, kana za a raya kasar Sin ta zamani mai karfi bisa tsarin gurguzu tun daga shekarar 2035 zuwa tsakiyar karnin da muke ciki. Ana sa ran cewa, jama’ar kasar Sin za su yi rayuwa mai dadi da wadata, kana za a iya warware matsaloli da dama bisa tunanin samun ci gaba dake la’akari da jama’a da farko. (Zainab)