logo

HAUSA

Ma’aikatar wajen Sin: Duk mai kaunar dukkanin duniya zai yi abokai a dukkanin sassan ta

2022-10-17 20:28:55 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yayin taron manema labarai na Litinin din nan cewa, shugabannin kasashen duniya da dama, da jagororin hukumomin kasa da kasa, sun aike da sakon taya murnar bude babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin(JKS) karo na 20, inda a sakwannin suka yi imanin cewa, karkashin jagorancin kwamitin kolin JKS da babban sakatarensa Xi Jinping a matsayin jigo, Sin za ta cimma nasarar farfado da kasa.

Wang Wenbin ya ce, "Duk mai kaunar dukkanin duniya zai yi abokai a dukkanin sassan ta". Ya ce tun bayan kammala babban taron wakilan JKS karo na 18, Sin ke nacewa hanyar samun ci gaba cikin lumana, da gina sabon salon cudanyar kasa da kasa bisa martaba juna, da gaskiya da adalci, da cimma moriyar juna, da goyon bayan gina al’ummar duniya mai makomar bai daya ga dukkanin bil adama.

Kaza lika har kullum kasar na kasancewa mai ingiza zaman lafiyar duniya, mai ba da gudummawa ga ci gaban kasa da kasa, mai ba da kariya ga tsarin gudanarwar kasa da kasa. Bugu da kari, Sin na gabatar da dabarun ta, da hanyoyin warware manyan matsalolin dake addabar duniya.

Wang Wenbin ya kara da cewa, kuri’un jin ra’ayin jama’a da dama, sun shaida yadda sassan duniya daban daban ke maraba da matsayar kasar Sin, musamman ma kasashe masu tasowa. Ga misali, babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya jinjinawa kasar Sin bisa yadda ta zamo kasa da ba za a iya yi ba ita ba, kuma amintaccen karfi na ingiza zaman lafiya da ci gaban duniya baki daya. (Saminu Alhassan)