logo

HAUSA

Yawan batura da ake amfani da su a motoci da kasar Sin ta samar ya zarce sama da kaso 101 a watan Satumba

2022-10-17 10:50:50 CMG HAUSA

 

Alkaluman da masana’antar kera motoci masu amfani da sabbin makamashi ta kasar Sin ta fitar na nuna cewa, yawan baturan dake samar da wutar lantarki da kasar Sin ta samar, sun karu cikin sauri a watan Satumba, a gabar da ake samun bunkasuwar motoci masu amfani da sabbin makamashi a kasuwar kasar.

A cewar kungiyar masu kera motoci ta kasar Sin, a watan da ya gabata, karfin baturan da aka samar ya karu da kaso 101.6 cikin dari bisa makamancin lokaci na bara, zuwa gigawatt 31.6 kan kowace sa’a (GMh). Bugu da kari, kasuwar motoci masu amfani da sabbin makamashi ta kasar Sin, ta ci gaba da bunkasa a cikin watan Satumba, inda aka samu karuwar cinikin motoci masu amfani da sabbin makamashin da kashi 93.9 cikin 100 a shekarar da ta gabata zuwa motoci dubu 708. (Ibrahim Yaya)