logo

HAUSA

Manyan jami’an jam’iyyun duniya da abokan kasar Sin sun taya murnar bude taron wakilan JKS karo na 20

2022-10-17 11:23:51 CMG HAUSA

 

Yayin da ake gudanar da taron wakilan jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 20, manyan jami’an jam’iyyun siyasa a sassan duniya, da abokan kasar Sin sun aika da sakwanni ga kwamitin tsakiya na JKS da babban sakataren JKS Xi Jinping, don taya murnar bude babban taron wakilan JKS karo na 20.

Shugaban jam’iyyar ANC ta kasar Afirka ta Kudu kuma shugaban kasar Matamela Cyril Ramaphosa ya bayyana cewa, ana gudanar da babban taron wakilan JKS karo na 20 a lokaci mai muhimmanci da kasar Sin da ma duniya ke tinkarar manyan sauye-sauye. Jam’iyyar ANC tana dora muhimmanci sosai kan sada zumunta dake tsakaninta da jam’iyyar Kwaminis ta Sin, kuma hadin gwiwa da burinsu iri daya, su ne tushe na kiyaye dangantakar dake tsakanin jam’iyyun biyu. Yayin da ake tinkarar sauye-sauyen da duniya fama da su, ya yi imanin cewa, jam’iyyun biyu za su yi amfani da dama da ma tinkarar kalubale tare, don sa kaimi ga raya dangantakar dake tsakanin jam’iyyun biyu. Kana ya yi fatan za a cimma nasarar gudanar da babban taron wakilan JKS karo na 20, da fatan za a samu muhimman sakamako a yayin taron, ta yadda hakan zai kai ga bunkasar jam’iyyar Kwaminis ta Sin tare da cimma burin da ta sanya gaba na samun wadata a kasar Sin baki daya.

Shi ma shugaban kasar Gabon Ali-Ben Bongo Ondimba ya taya murnar bude babban taron wakilan JKS karo na 20 cikin nasara, tare da yin imani da cewa, za a tsai da kudurori masu dacewa a yayin taron. Ya kara da cewa, bisa jagorancin jam’iyyar Kwaminis ta Sin, kasar Sin ta kasance daya daga cikin kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya, wadda ta kawowa jama’arta zaman lafiya da kwanciyar hankali da jin dadin rayuwa, don haka, ya jinjinawa jam’iyyar Kwaminis ta Sin bisa ga muhimmiyar rawa da take takawa game da harkokin da suka shafi kasar Sin baki daya. (Zainab)