logo

HAUSA

Wani Rahoton Aiki Mai Burgewa

2022-10-17 20:58:53 CMG Hausa

Rahoton da babban sakataren jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS) Xi Jinping ya gabatar a jiya Lahadi, a yayin bude babban taron wakilan JKS karo na 20 yana da burgewa sosai, saboda cike yake da bayanai masu nasaba da tunanin dora muhimmanci kan moriyar jama’a.

A cikin rahoton, yayin da ake bayyana nasarorin da jam’iyyar ta cimma a shekarun baya, an fi dora mihimmanci kan yadda ta kare rayuka da lafiyar al’umma daga cutar COVID-19, da kawar da talauci a kasar Sin, da kafa tsarin ilimi, da aikin lafiya, da ba da tabbaci ga ingancin zaman rayuwar jama’a mafi girma a duniya. Kana a bangaren ayyukan da za a yi a nan gaba, an jaddada bukatar daidaita matsalolin da suka fi damun jama’a, da samar da isassun damammakin raya kai.

Ban da bayanan rahoton, wasu wakilan JKS mahalartar taron, su ma sun shaidawa manema labaru, yadda tunanin dora muhimmanci kan moriyar jama’a yake yin amfani a kasar.

Zulyati Simayi, wakiliyar JKS ce da ta zo daga jihar Xinjiang ta kasar Sin. Ta yi bayani kan labarin wata yarinya ‘yar Uygur: Wannan yarinya da aka haifa a gundumar Wensu ta garin Aksu, bayan da ta kammala karatun sakandare, ta shiga makarantar koyar da ilimin sana’a, inda ta koyi fasahar hannu ta dinki domin kawata tufafi. Daga baya ta fara aiki a ma’aikatar samar da tufafi don neman inganta fasaharta ta dinki. Zuwa yanzu, bisa tallafin gwamnati, ta kafa wata ma’aikatar dinkin tufafi ta kanta, inda ta samar da dimbin guraben aikin yi ga matasa.

A nata bangare, Jiang Lijuan, matar dake rike da mukamin dagacin kauyen Xiajiang dake lardin Zhejiang na kasar Sin, ta yi bayani kan yadda mutanen kauyenta suke ta cimma burin samun karin kudin shiga. Ta ce a shekarar 2021, kudin shigar duk mutum daya a tsawon shekara a kauyenta ya kai dalar Amurka 6,522, jimillar da ta ninka ta shekarar 2003 har sau 14. Wannan lamari ya nuna yadda jam’iyyar mai rike da ragamar mulki a kasar Sin, wato JKS, take kokarin sanya ci gaban tattalin arzikin kasar a matsayin abun da zai amfani kowanne mutum na kasar.

Ko shakka babu, yadda ake mai da hankali kan moriyar jama’a, ya sa kasar ta Sin ta dora muhimmanci kan makomar bai daya ta daukacin bil Adama, ta fuskar manufar huldar kasa da kasa ta kasar. Wannan tunani shi ma yana cikin rahoton JKS dake kan karagar mulki a kasar.

A cewar Lin Zhanxi, wakilin JKS, kuma kwararre a fannin nazarin fasahohin aikin gona, shi da tawagarsa na kokarin yayata fasahar noman laimar kwado a duniya, bisa goyon bayan da gwamnatin kasar Sin ta ba su. Dalilin da ya sa ake yin haka, shi ne wannan fasaha ta taka muhimmiyar rawa, a kokarin kasar Sin na fid da manoma daga kangin talauci. Yanzu haka an horar da ma’aikata fiye da 12,000 a kasashe masu tasowa da dama, wadanda suka yada fasahar zuwa wasu kasashe da yankuna 106.

Ta wadannan misalai, ana iya ganin yadda JKS take kokarin kare moriyar jama’ar kasar Sin, gami da ta dukkan dan Adam, bisa babbar manufarta ta kokarin bautawa jama’a. Wannan manufar ita ce dalilin da ya sa ta samu damar rike ragamar mulki a kasar Sin har tsawon shekaru 73, kuma take ci gaba da samun goyon baya daga al’ummar kasar Sin. (Bello Wang)