logo

HAUSA

Jam'iyyun siyasa a Nijar sun taya murnar bude babban taron wakilan JKS karo na 20

2022-10-17 20:24:40 CMG Hausa

A yayin da babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20 ke gudana, jam'iyyun siyasar Nijar sun aike da wasiku, zuwa ga kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, da babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar Xi Jinping, domin taya murnar nasarar da aka cimma ta gudanar da babban taron.

Shugaban riko na jam'iyyar PNDS-Tarayya mai mulkin Nijar, kuma babban wakilin shugaban kasar, Foumakouye Gado ya bayyana cewa, a karkashin jagorancin babban sakatare Xi Jinping, kasar Sin ta samu gaggaruman nasarori a fannonin zamanantar da al'ummar kasar, kana ta taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya a duniya.

Ya ce, jam’iyyarsa tana taya murnar shirya babban taron wakilan JKS karo na 20 cikin nasara, kuma ta yi imanin cewa, taron zai kara inganta hadin kan al'ummar kasar Sin. Kaza lika PNDS-Tarayya na fatan karfafa hadin gwiwa da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, don kara kyautata 'yan uwantaka.

Shi kuwa a cikin ta sa wasikar taya murnar, shugaban jam'iyyar MNSD-Nassara, kuma shugaban majalisar dokokin kasar Seini Oumarou, ya taya jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin murnar jagorantar jarumtar jama'ar kasar Sin, wajen samun gagarumar nasarar 'yantar da kasa, da ci gaban tattalin arziki da zamantakewa. (Mai fassara: Bilkisu Xin)