logo

HAUSA

Tattalin arzikin kasar Sin na ci gaba da farfadowa a bana

2022-10-17 14:38:34 CMG HAUSA

 

Yau da safe ne, aka gudanar da taron manema labarai na farko a cibiyar watsa labarai ta babban taron wakilan JKS karo na 20. Taron ya gabatar da fara aiwatarwa da kafa sabon ra’ayin raya kasa, da sa kaimi ga samar da bunkasuwa mai inganci, gami da babban aikin farfado da daukacin al’ummar Sinawa da inganta burin farfado da kasar Sin mai sigar kasar Sin ta zamani.

A yayin taron manema labaran, mataimakin darektan hukumar raya kasa da zurfafa gyare-gyare Zhao Chenxin, ya gabatar da cewa, ko da yake tattalin arzikin kasar Sin ya fuskanci sauye-sauye a kowane wata tun daga bana, amma baki daya ya ci gaba da farfadowa da ma samun ci gaba.

Zhao Chenxin ya kara da cewa, tun daga wannan shekara, sakamakon tsaikon da duniya ke fuskanta sanadiyar annobar COVID-19, da mawuyacin halin da duniya ke ciki, da raunin zuba jari na kasashen ketare, duk da haka, jarin waje na kasar Sin ya samu sakamako mai gamsuwa da inganci. Kasar Sin za ta hada kai da bangarorin da abin ya shafa, don kara bude kofa ga kasashen ketare, da karfafa manufar jawo jarin waje.

A nasa bangare, mataimakin darektan hukumar kula da makamashi ta kasar Sin Ren Jingdong ya bayyana cewa, yayin da ake kara inganta ginshikin tattabar da samar da makamashi da ake iya sabuntawa, kasar Sin za ta kara inganta makamashin da ake iya sabuntawa da sa kaimi ga aiwatar da sauye-sauye da rage fitar da iskar carbon mai gurbata muhalli. (Ibrahim Yaya)