logo

HAUSA

Afirka ta kudu ta jinjinawa kasar Sin bisa kwazonta a fannin samar da ci gaba da zaman lafiya a duniya

2022-10-16 15:40:55 CMG Hausa

Babban sakataren jam’iyyar kwaminis a Afirka ta kudu Solly Mapaila, ya ce cikin sama da shekaru 20 da suka gabata, Sin da Afirka ta kudu sun gudanar da kyakkyawar alaka, wadda ta ci gaba da habaka sannu a hankali.

Sabon zababben babban sakataren jam’iyyar ta SACP ya kara da cewa, ko shakka babu, shugabannin nahiyar Afirka na iya koyi daga salon shugabanci mai dorewa na JKS.

Mr. Mapaila ya ce tabbas JKS ta dara sa’a, idan dai ana batu ne na aiwatar da manufofi, wanda hakan na da muhimmanci kwarai, kasancewar yana ba da damar gwada ci gaban da aka samu, kuma ta hakan ana iya samun abun koyi don gane da batun jagoranci. Ya ce tsarin gudanar da jagoranci na JKS ya cimma manyan nasarori, ta yadda sassa daban daban dake nahiyar za su iya yin koyi da shi, musamman ma bangarorin dake rajin kawo sauyi.

Daga nan sai Mr. Mapaila ya jaddada cewa, Sin ba batu take yi na fatar baki kadai ba, a duk lokacin da take magana kan tallafawa Afirka, inda ya kawo dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka a matsayin misalin hakan. (Saminu Alhassan)