logo

HAUSA

Kasar Sin ba za ta nemi yi wa kasashen duniya babakere ba

2022-10-16 13:14:56 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana yayin bude taron mambobin JKS karo na 20 a yau Lahadi cewa, kasarsa ba za ta taba neman yi wa kasashen duniya babakere ko fadada iko da yankunanta ba.

A cewarsa, kasar Sin ta tsaya ne tsayin daka, wajen adawa da duk wani nau’i na babakere da neman iko da yakin cacar baka da tsoma baki cikin harkokin gidan kasashe da kuma nuna fuska biyu. (Fa’iza Mustapha)