logo

HAUSA

An bude babban taron wakilan JKS karo na 20

2022-10-16 11:04:48 CMG Hausa

An bude babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin JKS karo na 20, da misalin karfe 10 na safiyar yau Lahadi a Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Wakilan jam’iyyar, gami da wadanda aka ba su goron gayyata na musamman sama da 2300 sun halarci taron, tare da wasu da ba ’yan jam’iyyar kwaminis din ba da sauransu. Za kuma a rufe taron a ranar 22 ga wata.

A wajen taron, za’a saurara, gami da duba rahoton aiki na kwamitin kolin JKS na 19, da duba rahoton aikin da kwamitin ladabtarwa na kwamitin koli na JKS na 19 ya gabatar. Kana, za’a amince da gyararren shiri na kundin ka’idojin jam’iyyar JKS, da kuma zabar membobin kwamitin kolin jam’iyyar da na kwamitin ladabtarwar jam’iyyar a sabon zagaye.

Jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin mai tarihin shekaru 101, ta shafe tsawon shekaru 73 tana kan karagar mulkin kasar Sin, wato tun kafuwar Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin. Babban taron wakilan jam’iyyar, gami da kwamitin kolinta, su ne hukumar koli ta jam’iyyar. A kan gudanar da babban taron wakilan jam’iyyar a duk bayan shekaru biyar.  (Murtala Zhang)