logo

HAUSA

Xi ya yi kira da a gina kasar Sin ta zamani mai bin tsarin gurguzu

2022-10-16 11:56:40 CMG Hausa

Yayin da aka bude babban taron JKS karo na 20 a yau Lahadi, shugaban kasar Xi Jinping ya yi kira ga dukkan mambobin JKS da su himmantu cikin hadin kai, wajen tabbatar da gina kasar Sin mai tsarin gurguzu ta zamani ta kowacce fuska.

Cikin rahoton da ya gabatar yayin bude taron, Xi Jinping ya ce taron ya zo ne a lokaci mai muhimmanci, kasancewar jam’iyyar da daukacin Sinawa daga dukkan kabilu, na kan wata sabuwar hanya ta gina kasar zuwa ta zamani mai bin tsarin gurguzu ta kowacce fuska, da kuma kokarin cimma buri na biyu lokacin da za a yi murnar cika shekaru 100 da kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin.

Taken taron shi ne, daukaka tsarin gurguzu mai sigar kasar Sin da aiwatar da tunanin gurguzu mai sigar kasar Sin a sabon zamani da ci gaba da daukaka babban ruhin da jam’iyyar ta kafu a kai da kasancewa cikin kwarin gwiwa da karin karfi, da daukaka muhimman ka’idojin jam’iyyar da samun sabbin nasarori da ci gaba da tabbatar da karfi da kuzarinta da himmantuwa cikin hadin kai wajen gina kasa ta zamani mai bin tsarin gurguzu ta kowacce fuska, tare da kara farfado da kasar ta kowanne bangare. (Fa’iza Mustapha)