logo

HAUSA

Xi Jinping: A tsaya ga raya sassan da suka shafi hada-hadar kudade kai-tsaye

2022-10-16 13:22:11 CMG Hausa

Shugaba Xi ya nuna cewa, ya dace kasar Sin ta raya ingantaccen tsarin tattalin arziki irin na kasuwa mai salon gurguzu, da tsayawa gami da kyautata babban tsarin tattalin arziki irin na gurguzu, da kara habaka tattalin arziki irin na gwamnati, da kuma karfafa gwiwa da jagorantar ayyukan raya tattalin arzikin da ba na gwamnati ba, ta yadda kasuwannin kasar za su kara taka muhimmiyar rawa wajen daidaita albarkatu, kuma gwamnatin kasar ita ma za ta kara taka rawarta.

Xi ya jaddada cewa, ya dace a raya tsarin sana’o’i irin na zamani, da maida hankali sosai kan raya sassan da suka shafi hada-hadar kudade kai-tsaye, da raya sabbin masana’antu, da gaggauta gina kasar Sin mai karfin yin kere-kere, mai karfin binciken sararin samaniya, mai karfin zirga-zirgar ababen hawa, mai karfin amfani da yanar gizo ta intanet, mai karfin fasahar sadarwar zamani da sauransu. Har wa yau, ya kamata a nuna azama wajen farfado da yankunan karkara daga dukkan fannoni, da nuna fifiko wajen samar da ci gaban ayyukan noma da yankunan karkara, da kara saurin raya kasar Sin mai karfin aikin noma.

Shugaba Xi ya kara da cewa, ana bukatar a ci gaba da habaka bude kofar kasar Sin ga kasashen ketare, da gagguta raya kasar mai karfin harkokin kasuwanci, da taimakawa ci gaban aiwatar da shawarar “ziri daya da hanya daya”, a wani kokari na kiyaye tsarin tattalin arzikin duniya, da huldar tattalin arziki, da kasuwanci dake kunshe da bangarori daban-daban. (Murtala Zhang)