logo

HAUSA

Xi ya gabatar da siffofin musamman na zamanintar da kasar Sin

2022-10-16 12:54:23 CMG Hausa

Shugaba Xi Jinping ya jaddada muhimmancin siffofi na musamman na zamanintar da kasar Sin, inda ya ce zamanintar da tsarin gurguzu ne karkashin shugabancin JKS.

Cikin rahoton da ya gabatar yayin bude taron mambobin JKS karo na 20, Xi Jinping ya ce, zamanantarwar ta kunshi wasu siffofi da suka yi daidai da na tsarin zamanintar da dukkan kasashe, sai dai, ta fi karkata ga wasu siffofi na musamman da suka fi dacewa da tunanin kasar Sin kadai.

Ya kara da cewa, zamanantar da kasar Sin, zamanantar da jama’a ne mai yawa da samar da ci gaba ga kowa, da ci gaban al’adu da zaman jituwa tsakanin dan Adam da sauran halittu da kuma samun ci gaba cikin zaman lafiya. (Fa’iza Mustapha)