logo

HAUSA

Tsarin demokaradiyyar da ya shafi kowa da kowa na kasar Sin

2022-10-16 18:54:42 CMG Hausa

An kaddamar da babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20 a yau Lahadi 16 ga wata. A cikin rahoton da ya gabatar a madadin kwamitin kolin jam’iyyar karo na 19, shugaba Xi Jinping ya nuna cewa: “Tsarin demokaradiyyar da ya shafi kowa da kowa, ainihin ma’ana ce ta siyasar demokuradiyya irin ta salon gurguzu, kana ainihin demokiradiyya ce mai amfani, wadda ta shafi baki dayan al’ummar kasar Sin.”

A kasar Sin, “demokuradiyya” ba ta samo asali daga tsohuwar kasar Girka ba, ta samo asali ne daga wani tsohon littafi mai suna Shangshu, dake bayyana tunanin babban masani Confucius sama da shekaru 2200 da suka wuce. Ma’anar kalmar “demokuradiyya” na nufin, a kan zabi sarki ko shugaba daidai bisa son al’umma. Wannan shi ne tunanin demokuradiyya na farkon farawa a kasar Sin, wanda ya aza tubali ga kafa tsarin demokuradiyyar da ya shafi kowa da kowa na kasar.

Bari mu dauki babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20 a matsayin misali, wanda ya shaida yadda kasar Sin take aiwatar da irin wannan tsarin demokuradiyya wanda ya shafi kowa da kowa. Da farko, wakilai 2296 da suke wakiltar dukkan ‘ya’yan jam’iyyar sama da miliyan 96, suna wakiltar muradun fannoni da bangarori daban-daban, ciki har da mata, ‘yan jam’iyyar, gami da ‘yan kananan kabilu.

Har wa yau, a watannin da suka gabata, jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ta fara aikin jin ra’ayin al’umma ta kafar intanet, dangane da ayyukan da suka shafi babban taron a wannan karo. Bugu da kari, kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, ya kira wani taro na mutanen da ba ‘yan jam’iyyar ba ne a birnin Beijing, inda aka saurari ra’ayoyi, da shawarwari daga wajensu, kan rahoton babban taro karo na 20 na jam’iyyar. (Murtala Zhang)