Shugaba Xi ya yi fashin baki game da muhimmin aikin JKS
2022-10-16 12:30:27 CMG Hausa
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi cikakken bayanai game da muhimmin aikin da JKS ke gudanarwa, a sabuwar tafiyar da ake yi cikin sabon karbi.
Shugaba Xi ya bayyana hakan ne a Lahadin nan, yayin da yake gabatar da rahoto, a wajen bude babban taron JKS na 20. Ya ce, "Tun daga yau, babban aikin dake gaban JKS, zai kasance jagorantar daukacin al’ummar Sinawa wajen zage damtse, domin cimma “Muradi na tsawon shekaru 100” da gina kasar Sin ta zamani mai bin salon gurguzu a dukkanin fannoni, tare da ingiza farfadowar kasar Sin daga dukkanin fannoni, ta hanyar bin salon kasar na zamanantar da kasar.
Shugaban na Sin ya kara da cewa, babban burin JKS shi ne cimma nasarar zamanantar da gurguzu tsakanin shekarar 2020 zuwa 2035, tare da gina kasar Sin ta zamani mai wadata, da karfi, da dimokaradiyya, da ci gaban al’adu, da hadin kai da kyau, daga shekarar 2035 zuwa tsakiyar wannan karbi. (Saminu Alhassan)