logo

HAUSA

Xi Jinping: Tattalin arzikin kasar Sin ya samu bunkasa da ba’a taba ganin irinta ba a tarihi

2022-10-16 12:45:16 CMG Hausa

An kaddamar da babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin JKS karo na 20 da safiyar yau Lahadi a Beijing, inda shugaba Xi Jinping ya gabatar da muhimmin rahoto, a madadin kwamitin kolin jam’iyyar na 19.

Shugaba Xi ya ce, a shekaru 10 da suka gabata, yawan GDPn kasar Sin ya karu daga kudin Sin Yuan tiriliyan 54, har zuwa tiriliyan 114, kana jimillar tattalin arzikin kasar Sin ta dauki kaso 18.5 bisa dari, na jimillar tattalin arzikin duk duniya, adadin da ya karu da kaso 7.2 bisa dari, wanda ya sa kasar ta zama ta biyu a duniya.

Shugaba Xi ya kuma ce, kasar Sin ta zama babbar aminiyar cinikayya ga kasashe da yankuna sama da 140, kuma jimillar kudin cinikayyar kayayyaki ta kasar tana kan gaba a duniya, kana, yawan jarin waje da kasar Sin ta jawo, da yawan jarin da ta zuba a sauran kasashe duk suna kan gaba. A halin yanzu kasar Sin tana habaka bude kofarta ga kasashen waje a fannoni daban-daban.

Xi ya kara da cewa, kasar Sin ta samu babban ci gaba wajen raya wasu muhimman fasahohi, da kara bunkasa sabbin sana’o’i da dama, ciki har da zirga-zirgar kumbuna masu dauke da dan Adam a sararin samaniya, da binciken duniyar wata da duniyar Mars, da binciken yankin ruwan teku mai zurfi, da nazarin manyan na’urori masu kwakwalwa, da taurarin dan Adam, da amfani da makamashin nukiliya don samar da wutar lantarki, da kera manyan jiragen sama, da harhada magunguna da sauransu, al’amarin da ya sa Sin ta shiga jerin kasashen dake kan gaba a duniya, wajen yin kirkire-kirkire. (Murtala Zhang)