logo

HAUSA

Xi Jinping: An cimma manyan nasarori cikin shekaru 5 da suka gabata

2022-10-16 12:09:36 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce an cimma manyan nasarori na ban mamaki cikin shekaru 5 da suka gabata, tun bayan babban taron wakilan JKS karo na 19 da ya gabata.

Shugaba Xi wanda ya bayyana hakan a Lahadin nan, yayin da yake gabatar da rahoto, a lokacin bikin bude babban taron wakilan JKS na 20. Ya ce kwamitin kolin JKS ya yi aiki tukuru, wajen cimma nasarorin farfado da kasa, a gabar da duniya ke fuskantar manyan kalubale, irin wadanda ba a ga kamar su ba cikin wannan karbi. Ya ce kwamitin koli ya yi rawar gani, wajen tsara managartan manufofin raya jam’iyya da ma kasa baki daya.

Shugaban na Sin ya kara da cewa, kwamitin kolin JKS, ya tattaro dukkanin sassan jam’iyya, da rundunar sojojin kasar Sin, da daukacin al’ummar Sinawa, ya kuma jagoranci sassan, wajen tunkarar manyan al’amura masu sarkakiya na ci gaban kasa da kasa, da ma jerin kalulabe masu tattare da hadurra dake shafar kasar.  (Saminu Alhassan)