logo

HAUSA

Hukumomi a Ghana sun bukaci a dage da tsaftar hannu domin kandagarkin COVID-19

2022-10-16 15:25:57 CMG Hausa

Shugabar shirin wayar da kan jama’a game da wanke hannu na gwamna kasar Ghana, Theodora Adomako-Adjei, ta bukaci al’umma su dage da kula da tsaftar hannu domin kandagarkin yaduwar annobar COVID-19 da sauran cututtuka masu yaduwa.

Theodora Adomako-Adjei, ta bayyana haka ne a jiya Asabar, a birnin Kumasi dake kudancin kasar, yayin da ake bikin ranar wanke hannu ta duniya.

A cewarta, an fara bikin ranar ne da dadewa, tun kafin bullar annobar COVID-19, kuma ya kamata a ci gaba da dabi’ar, tana mai kira ga jama’a da kada su dauke ta a matsayin ta kandagarkin COVID-19 kadai. (Fa’iza Mustapha)