logo

HAUSA

Kamfanonin Sin suna hayar ma’aikata a Zimbabwe

2022-10-15 15:53:35 CMG Hausa

Jiya Jumma’a ne, agogon kasar Zimbabwe, kamfanonin kasar Sin da wasu kamfanonin kasar Zimbabwe wadanda ke gudanar da hadin gwiwa da kamfanonin kasar Sin sama da 30, suka shirya taron daukar ma’aikata a birnin Harare, fadar mulkin kasar, inda aka samar da guraben aikin yi fiye da 700 ga daliban jami’a na kasar.

Kungiyar masu kamfanonin kasar Sin dake kasar Zimbabwe da bankin Standard na kasar ne suka shirya taron mai taken “Yin kokari tare domin ingiza ci gaban tattalin arzikin Zimbabwe” tare, inda aka samar da guraben aikin yi dake shafar bangarorin shari’a, da aikin kula da ma’aikata, da fassara, da saye da sayar kayayyaki, da fasahar sadarwa, da na injiniya da sauransu.

A halin yanzu kamfanonin kasar Sin dake gudanar da harkokinsu a Zimbabwe suna karuwa a kai a kai sakamakon ingantuwar hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a fuskokin tattalin arziki da cinikayya, da gina manyan gine-ginen more rayuwar jama’a, da cudanyar al’adu da kuma ba da ilmi, don haka ana bukatar karin ma’aikata na gari. Masu shirya taron hayar ma’aikatan, suna sa ran za su kara samar da guraben aikin yi masu inganci ga masu bukata a wurare daban daban na Zimbabwe, ta yadda za a ingiza hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Zimbabwe, tare kuma da farfado da tattalin arzikin kasar, ta yadda za a ciyar da huldar abokantaka dake tsakanin sassan biyu bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni gaba yadda ya kamata. (Jamila)