logo

HAUSA

Za a dawo da sufurin jiragen kasa tsakanin Abuja-Kaduna dake Najeriya

2022-10-15 16:38:01 CMG Hausa

Ministan sufurin Najeriya Mu’azu Sambo ya bayyana cewa, za a dawo da harkokin zirga-zirgar jiragen kasa tsakanin Abuja, babban birnin kasar da Kaduna dake yankin arewacin kasar, bayan an samar da matakan tsaro.

An dakatar da harkokin zirga-zirgar jiragen kasa ne, bayan da wasu ‘yan bindiga suka kaiwa jirgin kasan dake kan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Abuja ranar 28 ga watan Maris hari a garin Rijana dake jihar Kaduna, lamarin da ya haddasa mutuwar fasinjoji a kalla 8, wasu 26 kuma suka jikkata, kana aka yi awon gaba da sama da mutane 60.

Ministan ya bayyana cikin wata sanarwa da aka fitar a Abuja cewa, matakan tsaron da za a dauka, za su hada wasu tsare-tsare na gajere da dogon lokaci, da kuma wasu shirye-shirye masu gajerun wa’adi, kuma za su fara aiki ne daga watan Nuwamba mai kamawa. Ya kuma ce, suna duba yadda layukan dogo za su kasance cikin tsaro ta hanyar sanya ido ba dare da rana, baya ga na’urorin mayar da martani na gaggawa da za a tanada.

A cewar gwamnatin Najeriya dai, jimillar fasinjoji 362 da ma’aikatan jirgan kasa 20 ne suke cikin jirgin, a lokacin da aka kai masa harin.

A ranar 29 ga watan Maris, kwana guda da aukuwar harin, hukumar jiragen kasan Najeriya, ta sanar da dakatar da harkokin zirga-zirgar jiragen kasa tsakanin Abuja zuwa Kaduna har illa masha Allah. (Ibrahim)