logo

HAUSA

MDD: Kungiyoyin matasa masu dauke da makamai sun sake kaddamar da wani kazamin fada a Sudan ta kudu

2022-10-15 16:36:46 CMG Hausa

Farhan Haq, mai magana da yawun babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya bayyana cewa, dakarun dake aikin wanzar da zaman lafiya a kasar Sudan ta kudu, sun nuna damuwa matuka game da fadan da ake gwabzawa tsakanin matasan kabilar Dimka biyu masu dauke da makamai a arewacin kasar.

Haq ya bayyana cewa, an sake samun barkewar kazamin fada tsakanin ‘yan kabilar Dinka Ngok da Dinka Twic Mayardit a kan iyakar yankin Abyei dake tsakiyar kasar. Rikicin dai ya fara ne tun a watan Fabrairu, amma ya dan lafa a watan Yuni.

Ya kara da cewa, rikicin ya haddasa asarar rayuka da dama tare da lalata gidaje, baya ga raba dubban fafaren hula da matsugunansu.

Ya bayyana cewa, dakarun UNMISS dake aikin wanzar da zaman lafiya, suna sintiri a yankin tare da tattaunawa da mahukuntan yankin, da mata da shugabannin matasa. Haka kuma tawagar ta yi maraba da matakin da gwamnatin ta dauka na gudanar da bincike kan rikicin, tare da tura sojoji zuwa yankin domin maido da zaman lafiya. (Ibrahim)