logo

HAUSA

Xi ya mika sakon alhini ga Buhari game da hadarin nutsewar jirgin ruwa da ya auku a kasar

2022-10-15 15:57:40 CMG Hausa

A ranar 13 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isar da sakon alhini ga takwaransa na Nijeriya Muhammadu Buhari, bisa abkuwar hadarin nutsewar jirgin ruwa da ya faru a kasar.

Xi Jinping ya ce, ya kadu da samun labarin hadarin da ya auku a jihar Anambra dake kasar Nijeriya, wanda ya haddasa rasuwar mutane da dama. Don haka, a madadin gwamnatin kasar Sin da ma jama’arta, yana mika ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon hadarin, tare da jajantawa iyalansu. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)