logo

HAUSA

Kasar Sin ta harba sabon tauraron dan-Adam da ake iya sarrafa shi daga nesa

2022-10-15 16:33:18 CMG Hausa

Kasar Sin ta yi nasarar harba wani sabon tauraron dan-Adam da ake iya sarrafawa daga nesa zuwa sararin samaniya, daga cibiyar harba tauraron dan-Adam ta Xichang dake lardin Sichuan a yankin kudu maso yammacin kasar.

An dai yi amfani da rokar Long March-2D wajen harba tauraron samfurin Yaogan-36 da misalin karfe 3 da mintuna 12 a safiyar ranar Asabar agogon birnin Beijing, kuma ya shiga falakinsa cikin nasara.

Wannan shi ne karo na 444, da aka yi amfani da rokar Long March, wajen aikin harba kumbuna zuwa sararin samaniya.(Ibrahim)