logo

HAUSA

Al’ummar Sin mai matsakacin wadata da aka gina tana da inganci matuka

2022-10-15 20:47:18 CMG Hausa

Sun Yeli, mai magana da yawun babban taron wakilan JKS karo na 20, ya bayyana a yau cewa, kasar Sin ta gina al’umma mai matsakacin wadata da ta dara hasashen da aka yi a farkon aiwatar da manufar yin gyare-gyare da bude kofa. Ya kuma bayyana cewa, manufar gano annobar COVID-19 da kuma dakile ta nan da nan, ta dace da yanayin kasar da ma dokoki na kimiya. (Ibrahim)