logo

HAUSA

Za a wallafa rahoton Xi mai taken “Nacewa kan manufar mayar da jama’a a gaban kome” a mujallar Qiushi

2022-10-15 15:46:14 CMG Hausa

Gobe Litinin 16 ga wata ne za a wallafa wani muhimmin rahoto mai taken “Nacewa kan manufar mayar da moriyar jama’ar kasa a gaban kome” a mujallar Qiushi wanda babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, shugaban kasar kuma shugaban kwamitin aikin soja na kasar Xi Jinping ya rubuta.

Rahoton ya jaddada cewa, jama’ar kasar Sin, su ne tushen jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma nacewa kan manufar mayar da moriyar jama’ar kasa a gaban kome, ya nuna imani da buri na jam’iyyar.

Rahoton ya yi nuni da cewa, jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ba ta da moriyar musamman, a ko da yaushe tana mayar da moriyar al’ummun kasa ne a gaban kome. Wannan wata alama ce dake nuna bambancin dake tsakaninta da sauran jam’iyyu na sauran kasashe.

Kana rahoton ya bayyana cewa, makasudin raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma a kasar Sin shi ne domin biyan bukatun jin dadin rayuwa na al’ummun kasar, don haka ya dace a mai da hankali kan bukatun al’ummun kasa a ko da yaushe, alal misali samar da guraben aikin yi, da ba da ilmi, da samar da inshorar kiwon lafiya da gidajen kwana, da tabbatar da ingancin abinci da kwanciyar hankali da sauransu. (Jamila)