logo

HAUSA

An kaddamar da tsarin biyan kudi na zamani tsakanin Rwanda da Sin

2022-10-15 20:36:07 CMG Hausa

Babban bankin kasuwancin kasar Rwanda dake bayar da rance, wato Bank of Kigali da Ant Group, daya daga manyan masu samar da hidimar fasaha ga kasuwancin kasar Sin, sun kaddamar da hidimar biyan kudi daga Rwanda zuwa kasar Sin ranar Alhamis din da ta gabata a Kigali, babban birnin kasar.

Ana sa ran hidimar wadda ke karkashin harkokin kudi kamar yadda yake kunshi cikin tsarin cinikayya ta zamani na kasa da kasa, za ta bunkasa harkokin kasuwanci tsakanin kasashen biyu. (Ibrahim)