logo

HAUSA

INEC ta yiwa masu kada kuri’a miliyan 95 rajista gabanin zaben 2023

2022-10-14 09:49:56 CMG Hausa

Hukumar zabe mai zaman kanta a tarayyar Najeriya INEC, ta ce ta yiwa masu kada kuri’a miliyan 95 rajista, gabanin babban zaben kasar da za a gudanar a farkon shekara mai zuwa.

Da yake bayyana hakan cikin wata sanarwa a jiya Alhamis, shugaban hukumar ta INEC Mahmood Yakubu, ya ce cikin ’yan kwanakin nan ne aka kammala tattara bayanan masu kada kuri’ar ta amfani da na’urorin zamani, inda aka tantance hotunan ’yan yatsu da na fuskokin wadanda suka cancanci yin zabe, wadanda yawansu ya dara miliyan 95, adadin da ya haura miliyan 84 da aka yiwa rajista gabanin zaben shekarar 2019.

Kaza lika shugaban hukumar zaben ya ce a yanzu haka, akwai jam’iyyun siyasa 18 da za su fafata a zaben shugaban kasa, zaben da ya bayyana a matsayin mai matukar muhimmanci ga Najeriya.

INEC ta ayyana ranar 25 ga watan Fabarairun shekarar 2023, a matsayin ranar gudanar da zaben shugaban kasa da ’yan majalissun tarayya, yayin da kuma za a gudanar da zaben gwamnoni da ’yan majalissun jihohi, mako guda bayan na shugaban kasa. (Saminu Alhassan)