logo

HAUSA

Tsarin Gwamnatin Sin Na Ba Da Jiyya Ga Dukkanin Kauyuka Na Baiwa Al’Umma Kariya A Fannin Ba Da Jiyya

2022-10-14 19:26:39 CMG HAUSA

Daga MINA

Abokai, ko akwai wahalar samun jiyya a wuraren dake da nisa daga birane a wurin ku? Tun kafuwar jam’iyyar jama’ar kasar Sin, gwamnatin kasar na kokarin daidaita wannan matsala. Yau ma “Duniya a zanen MINA” na bayyana muku tsarin gwamnatin Sin na ba da jiyya ga dukkanin kauyuka.

  Saurayin dake cikin zanena sunansa Abdukrem Marghulam, ya kammala karatu kyauta bisa tallafin gwamnati a fannin ilmin likitanci a watan Yuli, kuma an tura shi zuwa kauyen Kokbash dake garin Baishtugman, na birnin Aksu dake jihar Xinjiang, a matsayin likitan wurin.

A wasu wuraren dake da nisa da birane kamar wannan kauye, ba su da isassun likitoci da magunguna, kuma al’ummar wurin ba su da damar samun jiyya. Domin warware irin wannan matsala, gwamnatin kasar Sin na daukar wasu matakai masu dacewa, ciki hadda rarraba albakatun ba da jiyya yadda ya kamata a wurare daban-daban, da daga matsayin ba da jiyya a wurare daban-daban, da kyautata hukumomin ba da jiyya a wuraren, da habaka ingancin masu aikin jiyya a wuraran da dai sauransu, ta yadda za a tabbatar da cewa, ana samar da jiyya ba tare da gamuwa da matsala ba.

   Shirin horar da likitoci kyauta, daya ne daga cikin wadannan matakai, kuma ya zuwa yanzu, ana horar da dalibai fiye da dubu 70 a wannan fanni, kuma daga cikinsu dalibai kimanin dubu 35 sun kammala karatunsu, an kuma tura su kauyuka daban-daban don zama likitoci.

A bana a jihar Xinjiang, matasa 229 kamar Abdukrem Marghulam da suka samu ilmin likitanci kyauta karkashin shirin gwamnati, sun tafi kauyuka daban-daban na jihar. Wadannan matasa sun ci gajiyar wannan shirin gwamnati sosai. Ba ma kawai sun samun aikin yi karkashin wannan shiri ba, har ma sun taka rawarsu wajen daga karfin ba da jiyya a kauyuka.

  Ya zuwa karshen shekarar 2021, kasar Sin ta kafa hukumomin jiyya a duk fadin kasar. Manoman kasar Sin suna iya samun jiyya a cikin kauyensu, matakin da kyautata zaman rayuwarsu.

Abokai, gwamnatin kasar Sin na mai da moriyar al’ummarta a gaban komai, da kokarin warwaren matsalolinsu da kawar da wahalhalunsu. Ba shakka za ta samu amincewa daga al’ummarta. (Mai zane kuma mai rubuta: MINA)