logo

HAUSA

Jakadan Sin A Najeriya Ya Halarci Dandalin Abuja Na 2022

2022-10-14 11:37:02 CMG Hausa

Jakadan kasar Sin a Tarayyar Najeriya Cui Jianchun, ya bayyana cewa, huldar da ke tsakanin Sin da Najeriya na ta bunkasa a shekarun baya-bayan nan, kuma sassan 2 na kara inganta amincewar juna ta fuskar siyasa, kana hadin gwiwarsu ta fuskar tattalin arziki, ya haifarwa jama’ar su alherai.

Baya ga haka kuma, kasashen 2 sun rika kyautata taimakawa juna ta fuskar tsaro tsakanin kungiyoyin kasa da kasa, tare da yin mu’amalar al’adu a tsakaninsu. Ya ce kasar Sin na son ci gaba da aiwatar da manyan tsare-tsaren ci gaba da bunkasa na 5GIST tsakaninta da Najeriya, bisa ra’ayi daya da shugabannin kasashen 2 suka cimma.

Cui Jianchun ya fadi haka ne a yayin da yake halartar taron dandalin tattaunawar Abuja ta shekarar 2022 ta kafar bidiyo a ranar 13 ga wata.

Mahalarta taron sun yaba da huldar da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka, sun kuma amince da manyan nasarorin bunkasuwa da kasar Sin ta cimma, karkashin shugabancin Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin. A ganinsu, shawarwarin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar dangane da bunkasar duniya da tsaron duniya, da kuma yadda ya jaddada ruhin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka, a yayin taron ministoci karo na 8 na dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka, sun ba da jagoranci kan hadin kai a tsakanin sassan 2 a mataki na gaba.

An kafa dandalin tattaunawar Abuja a shekarar 2018, wanda kwalejin nazarin Afirka ta jami’ar horar da malamai ta Zhejiang, da cibiyar nazari ta Gusau ta Najeriya suke gudanarwa cikin hadin gwiwa a duk bayan shekaru 2.

A bana, an gudanar da taron karo na 3, wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen yin mu’amala a tsakanin kwararru na Sin da Afirka. Wasu tsoffin jami’an gwamnatoci da kwararru daga Sin, da Najeriya, da Kenya, da ‘yan kasuwa, da ‘yan jarida sun tuntubi juna, da yin mu’amala a fannonin zaman lafiya, da tsaro, da rage talauci, da kawo wa manoma alheri, da sa kaimi kan yin ciniki, da yin kirkire-kirkire da fasahar zamani da dai sauran. (Tasallah Yuan)