logo

HAUSA

Za a gudanar da babban taron wakilan JKS karo na 20 a ranar 16 ga wata

2022-10-14 20:28:09 CMG Hausa

A safiyar ranar 16 ga wata da misalin karfe 10 ne, za a gudanar da babban taron wakilan JKS karo na 20, a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

A yayin taron, babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) da Xinhuanet, za su watsa abubuwan dake gudana kai tsaye. (Ibrahim)