logo

HAUSA

An yi kira ga matasan Afirka da su kara azamar ingiza ci gaban nahiyar

2022-10-14 12:39:33 CMG Hausa

An yi kira ga matasan Afirka, da su kara kwazo wajen ingiza manufofin ci gaban nahiyar Afirka. A cewar mahalarta taron “YouthConnekt” da ya kammala a birnin Kigalin kasar Rwanda a jiya Alhamis, matasa su ne kashin bayan ci gaban Afirka, don haka ya zama wajibi su mara baya ga wannan tafiya yadda ya kamata.

Cikin jawabinsa ta kafar bidiyo, shugaban kasar Namibia Hage Geingob, ya ce matasan Afirka su ne makomar wannan babbar nahiya. Kuma kasashen nahiyar da gwamnatocinsu, na dogaro ga irin gudummawa ta daidaiku da ma gamayyar tallafin matasa, ta yadda za a kai ga cimma muradun bunkasar Afirka cikin lumana.

A nasa jawabin, shugaban kasar Senegal Macky Sall, wanda kuma shi ne shugaban karba-karba na kungiyar AU na bana, cewa ya yi matasan Afirka su ne babban jarin nahiyar a yanzu da ma nan gaba.

Shi kuwa shugaban kasar Rwandan Paul Kagame ya ce, kamata ya yi a dauki matasa a matsayin abokan tafiya, cikin ajandojin samar da ci gaban kasashen Afirka.

Taron na yini 2 ya samar da damar sada matasa daga dukkanin sassan Afirka da ma tsallaken nahiyar da juna, ya kuma gudana karkashin jigon "Gaggauta zuba jari kan matasa: Juriyar matasa ita ce jurin Afirka". (Saminu Alhassan)