logo

HAUSA

Sin tana goyon bayan matakan da Afirka ke dauka game da sauyin yanayi

2022-10-13 19:35:56 CMG Hausa

A kwanakin baya ne, babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya yi kira ga kasashen duniya da su taimakawa kasashen Afirka, ta yadda za su tinkari matsalar sauyin yanayi.

A yayin taron manema labarai da aka saba shiryawa Alhamis din nan, mai magana da yawun ma’aikatar harkoki wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana cewa, “Mun lura da kalaman Guterres. Kuma kasar Sin tana tsayawa tsayin daka ba kuma tare da yin kasa a gwiwa ba wajen agazawa matakan da Afirka ke dauka game da matsalar sauyin yanayi.” (Ibrahim)