logo

HAUSA

Kyan Alkawari Cikawa

2022-10-13 16:09:23 CMG Hausa

Yanzu haka ana daf da cika shekaru 10 tun bayan taron farko na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin na 18, tun bayan lokacin ne kuma sassan kasa da kasa ke zuba ido domin ganin yadda kasar Sin za ta dunkule tare da sauran sassan duniya, wajen cika alkawuran da ta dauka, na samarwa al’ummar duniya kyakkyawar makomar bai daya.

A iya cewa a bisa dukkanin shaidu “Kwalliya ta biya kudin sabulu”, domin kuwa kasar Sin ta shiga cikin hadakar kasashen duniya, wajen aiwatar da managartan shirye-shiryen samar da ci gaba, duk kuwa da kalubalen da duniya ta ci karo da su cikin wadannan shekaru.

Yayin ziyararsa ta farko a kasashen waje cikin watan Maris na shekarar 2013, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya zayyana burin kasarsa na bunkasa sabon salon cudanya, da hadin gwiwa da sauran sassan duniya, ta yadda za a kai ga cimma moriyar juna, wanda dukkanin bil adama zai ci moriyarsa.

Cikin shekarun baya bayan nan, kowa ya ga yadda kasar Sin ke kara azamar sauke nauyin dake wuyanta, na ingiza samar da ci gaba cikin lumana, da goyon bayan cudanyar sassa daban daban bisa adalci.

Sakamakon haka, mun ga yadda Sin ke ci gaba da ba da gudummawa a ayyukan wanzar da zaman lafiya da daidaito, da ba da gudummawar bunkasa raya tattalin arzikin duniya, da shiga ayyukan cimma moriyar bil adama na bai daya.

Tuni manufar dake kunshe cikin shawarar nan ta “Ziri Daya da Hanya Daya” ko BRI, ta shiga lungu da sassan duniya, inda ta samar da zarafi karfafa kawance, da dinkewar Sin da sauran sassan duniya a fannin samar da ci gaba. Kaza lika Sin ta shiga ayyukan yaki da annobar COVID-19, ta samar da gudummawar kayan kandagarki da na rigakafin annobar, matakin da ya samu babban yabo daga sassa daban daban.

Duba da wadannan shaidu na zahiri, muna iya cewa, Sin ta cika alkawuran da ta dauka ga duniya, musamman ma ga kawayen ta makusanta wato kasashe masu tasowa. (Saminu Hassan)