logo

HAUSA

Wakilan babban taron wakilan JKS karo na 20 sun fara isowa birnin Beijing

2022-10-13 19:04:28 CMG Hausa

Yau ne, wakilai daga yankin Mongoliya ta gida dake yankin arewacin kasar Sin, da za su halarci babban taron wakilan JKS karo na 20 suka iso birnin Beijing.

Kuma su ne tawaga ta farko daga wajen birnin Beijing da ta iso fadar mulkin kasar, don gudanar da taron, wanda za a bude a ranar 16 ga watan Oktoban da muke ciki.

Sama da wakilai dubu 2 da 200, dake wakiltar fiye da mambobin JKS miliyan 96 a fadin kasar ne, za su halarci taron da ake gudanarwa bayan shekaru biyar. (Ibrahim)