logo

HAUSA

Sin ta harba sabon tauraron dan Adam na nazarin yanayi

2022-10-13 10:55:39 CMG Hausa

Da sanyin safiyar Alhamis din nan ne kasar Sin ta yi nasarar harba tauraron dan Adam na aikin lura da yanayi, da ayyukan rage aukuwar bala’u, da aiwatar da matakan gaggawa masu nasaba da yanayi da dai sauransu.

An harba sabon tauraron samfurin S-SAR01 ne daga cibiyar harba kumbuna ta Taiyuan, wadda ke lardin Shanxi na arewacin kasar da karfe 7 saura mintuna 7 na safe, ta amfani da rokar Long March-2C. Tuni kuma tauraron ya shiga falakin sa kamar yadda aka tsara. Kaza lika sassan da za su yi amfani da ingantattun hotuna da bayanan da tauraron zai samar, sun hada da ma’aikatar lura da ayyukan gaggawa, da ma’aikatar lura da muhalli da dangantakar muhallin da halittu.

A cewar hukumar lura da harkokin sararin samaniya ta kasar Sin, sabon tauraron zai taka rawar gani, wajen samar da bayanan da za su taimakawa ayyukan kandagarki, da rage tasirin bala’u, da kuma kare muhalli. Kaza lika zai ba da damar lura da albarkatun kasa, da kare ingancin ruwa, da bunkasa noma, da kula da gandun daji, da girgizar kasar, da sauransu.

Wannan ne karo 443 da aka yi amfani da rokar Long March, a aikin harba kumbuna a kasar Sin.  (Saminu Alhassan)