logo

HAUSA

Kwallon kafa na tallafawa ‘yan mata marasa galihu a Zimbabwe

2022-10-13 21:00:04 CMG Hausa

Daga yankin Hatcliffe mai filin wasa na marasa galihu, a bangaren unguwar talakawa dake wajen birnin Harare fadar mulkin kasar Zimbabwe, wasu ‘yan wata 10 za su daga tutar kasar Zimbabwe, a gasar cin kofin kwallon kafa ta yara da za a buga a kasar Qatar, tsakanin ranekun 8 zuwa 15 ga watan Oktobar nan.

Wadannan ‘yan mata da suka ratso yanayi na rashin daidaiton jinsi da fatara, da wahalhalun rayuwa, a wannan lokaci, sun samu damar shiga a dama da su a gasar kasa da kasa mai kunshe da kulaflika 28, daga kasashe da yankuna 24.

Wannan gasa ta kwallon kafar yara, wata dama ce ta sada zumunta tsakanin yara matasa daga sassa daban daban na duniya, cikin jerin ayyuka da ake gudanarwa, albarkacin gasar cin kofin duniya da hukumar FIFA ke shiryawa.

Yayin da suke barin kasar su, matashiya Amy Karasa na cike da murmushi. Karasa ta bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa "Na yi farin ciki kasancewar zan wakilci Zimbabwe a Qatar, domin mutane kalilan ne ke iya samun irin wannan dama. Wannan dama ce kalilan a rayuwa, dama ce mai iya canza rayuwar mutum".

A nata bangare kuwa, Ruth Chantel James, cewa ta yi samun zarafin wakiltar kasar ta a wannan gasa ta kasa da kasa, mafarki ne da a yanzu ya zamo gaskiya.

Ta ce "Mafarki na shi ne wata rana na fita wajen wannan kasa ta mu, na je wani wurin na daban, na wakilci Zimbabwe, na wakilci ‘yan matan Zimbabwe, kana na daga darajar al’ummun dake yankuna marasa galihu, a matsayin misali ga sauran al’ummun mu. Zan wakilci dukkanin ‘yan mata dake yankin mu, zan kuma muna musu cewa, ba wani abu da ba za su iya yi ba. A matsayin mu na ‘yan wannan yanki, muna fuskantar kalubale masu yawa. Wasu lokuta idan muka zo buga kwallo, sai mun manta da abubuwa da dama na gida, sannan zuciyar mu za ta nutsu, sai mu hadu da juna, mu yi cudanta, mu yi musatar ra’ayoyi, mu warware matsaloli, kana mu taimakawa juna a lokacin da muke tare".

Ita ma Gamuchirai Tsabora, fatan ta shi ne fatatawa a babbar gasa da za ta sauya rayuwar ta. Ta ce "Ina cike da farin ciki. Buga kwallon kafa yana sa ni nishadi. Ni ce ta farko cikin iyalin mu da zan shiga jirgin sama, don haka zan tashi cikin farin ciki. Ina son bayyana cewa, wasan kwallon kafa abu ne mai kyau, saboda ya daga martaba ta. Ban taba zaton zan fita kasar waje ba, amma yanzu na cimma wannan buri ta hanyar kwallon kafa".

Ita ma mahaifiyar ta Pamela Zivare, tana cike da farin ciki, inda ta ce "Ina farin ciki da nasarar ‘ya ta. Ina fatan da wannan nasara ta ta, za ta daga matsayin rayuwar iyalin mu, don haka ina cike da murna da nasarar Gamuchirai".

A nata bangare, babbar manajar sashen raya wasannin matasa ta Zimbabwe ko YASD, Pearl Gambiza, ta ce wasanni na karfafa gwiwar matasa, ta yadda za su kai ga cimma burikan su, daga wasanni a kan tituna zuwa buga wasan cin kofin duniya, wato dai tamkar wata dama ce ta daga martabar rayuwar yara musamman na yankuna marasa galihu.

Game da wannan dama da Zimbabwe ta samu, kocin ‘yan matan Mercy Humbira ta ce "Ga wadannan ‘yan mata, wasun su suna shirin ci gaba zuwa buga wasannin ajin kwararru, wasu suna son zama masu horas da ‘yan wasa, don haka wannan wata dama ce gare su, ta ingiza niyar su zuwa sana’oi daban daban masu nasaba da kwallon kafa”. Mercy Humbira ta ce tana da kwarin gwiwar cewa, ‘yan wasan ta za su cimma manyan nasarori.

Koci Humbira ta kara da cewa, "A matsayin wadanda suka fito daga yankin Hatcliffe, wuri mai fama da talauci, muna zaune a gidaje marasa inganci, yanzu ina farin cikin ganin wadanda ake wa kallon kaskanci sun kai kololuwar matsayi, na wakiltar Zimbabwe, kuma ina da kwarin gwiwar cewa, za mu yi nasara saboda mun yi aiki tukuru".

Humbira na ganin cewa, kwallon kafa na budewa yaran ta damammaki masu yawa. Ta ce "Kwallon kafa ta daga matsayin yaran, saboda mutane da yawa daga wannan yanki na mu ba sa zuwa makaranta. Iyayen su ba su da aiki na zamani, ba su da kudaden shiga na yau da kullum, amma ta hanyar taka leda, muna nunawa duniya irin basirar mu.

Ga sauran yara kamar su Ropafadzo Kamuruku, wannan dama ce ta kawar da rashin daidaiton jinsi da suka fuskanta. Domin kuwa duk da cewa da farko mahaifin ta bai gamsu da zabin ta na buga kwallon kafa ba, a yanzu shi ne ya fi kowa nuna mata goyon baya. Ta ce "Lokacin da Baba na ya lura cewa na iya taka leda sosai, sai ya je ya yi magana da kocin mu, ya ce mata wannan wani ci gaba ne, ya ce zan iya kwallo, zan iya kaiwa wurare da yawa ta hanyar kwallo, a yanzu yana son saya min kayan wasa, yana karfafa min gwiwar buga kwallon kafa. Ga sauran yara mata da ake nuna shakku game da yadda suke buga kwallo, ina kira gare su da su dage wajen nuna basirar su, domin wasa ne na kowa da kowa. Idan kina son buga kwallo ki zo fili, za mu taimaka maki, za ku iya cimma nasarori sosai kamar yadda na cimma"

Kamar dai ra’ayin Kamuruku, ita ma Karasa, cewa ta yi kwallon kafa ba na maza ba ne kawai. Karasa ta ce "Ina ganin har yanzu mutane na kallon rayuwa kamar a da can, lokacin da mata ke fuskantar nuna banbanci kan abun da maza ke iya yi. Don haka ina ga mutane na nacewa yanayin rayuwar lokacin da, maimamkon rungumar zamanin yau”.

Babbar manajar sashen raya wasannin matasa ta Zimbabwe ko YASD, Pearl Gambiza, ta kara da cewa, shigar yara mata cikin harkokin wasanni, zai ba su damammaki masu yawa, ciki har da karfin gwiwar yin abubuwa da yawa na bunkasa rayuwa, da kawar da su daga shiga muggan abubuwa, musamman masu bata rayuwar yara a yankuna matalauta.

Gambiza ta ce "Maimakon zaman banza, akwai abubuwan yi masu yawa, kamar atisaye, da gwada kwarewa, wadanda ke taimakawa yara wajen kaucewa munanan dabi’u ta hanyar cudanya da abokai”.

A wurare masu fama da talauci, rashin damammakin raya tattalin arziki, na haifar da zaman-kasha-wando tsakanin matasa, wanda hakan ke sanyawa a shiga aikata laifuka, da shan miyagun kwayoyi, da auren wuri.