logo

HAUSA

Kwamitin musamman na ECOWAS ya bukaci a karfafa goyon baya ga masu bukatu na musamman

2022-10-13 14:12:29 CMG Hausa

Kwamitin nazari na kungiyar bunkasa tattalin arzikin Afirka ECOWAS, ya yi kira da a karfafa mara baya ga sha’anin mutane masu bukata ta musamman.

Mambobin kwamitin sun fitar da sanarwar bayan taron yini 3 da suka gudanar a jiya Laraba, inda a ciki suka jaddada bukatar baiwa rukunin mutane masu bukatar musamman cikakkiyar damar jagorantar hukumomi, da ayyukan da suka shafe su. Kaza lika a samar musu damar wakiltar kasashensu a tarukan ECOWAS masu nasaba da su, kana ECOWAS ta karfafa damar shigar da kwararru masu bukatar musamman cikin harkokin shiyyar.

Cikin sanarwar bayan taron ta kwamitin nazarin na kungiyar ECOWAS, mai kunshe da mambobin shiyyar 15, an bayyana muhimmancin amincewar dukkanin mambobin ECOWAS, da kudurin kungiyar tarayyar Afirka AU game da kare hakkokin masu bukatar musamman, tare da shigar da su cikin harkokin al’umma.

Kudurin dai tanadin doka ne, mai baiwa mambobin kungiyar AU zarafin tsara dokoki da manufofi, na inganta harkokin masu bukata ta musamman a kasashen shiyyar. (Saminu Alhassan)