logo

HAUSA

Ministocin lafiyar kasashen Afirka 11 sun yi taro game da barkewar cutar Ebola a Uganda

2022-10-13 10:12:40 CMG Hausa

Ministocin lafiyar kasashen Afirka 11, sun gudanar da taro game da barkewar cutar Ebola a kasar Uganda. Da yake bayyana manufar taron na jiya Laraba, jagoran ofishin hukumar kiwon lafiya ta WHO a Uganda, ya ce ministocin sun tattauna game da bukatar yin hadin gwiwar kimtsawa, da aiwatar da matakan dakile bazuwar cutar ta kan iyakokin Uganda.

Mashirya taron, da suka hada da ma’aikatar lafiya ta Uganda, da kungiyar tarayyar Afirka ta AU, da cibiyar kandagarki da yaki da cututtuka ta Afirka, da hukumar WHO, sun ce suna fatan taron zai share fagen karfafawa, da inganta hadin gwiwar yaki da cutar ta Ebola mai haifar da zubar da jini, da ma sauran larurorin lafiya na gaggawa a Afirka.

Taron dai ya samu halartar manyan jami’an hukumar WHO, karkashin jagorancin Michael Ryan, da babban daraktan sashen ayyukan gaggawa na hukumar.

Kasar Uganda na fuskantar bazuwar annobar Ebola nau’in kasar Sudan, tun bullar ta a karon farko a yankin tsakiyar kasar a ranar 20 ga watan Satumba. Alkaluman ma’aikatar lafiyar kasar sun nuna cewa, ya zuwa ranar Lahadi 9 ga watan nan, adadin wadanda aka tabbatar sun harbu da cutar ya kai mutum 48, yayin da tuni ta hallaka mutane 17. (Saminu Alhassan)