logo

HAUSA

Bambancin yawan kudin shiga tsakanin mazauna birane da na yankunan karkarar Sin ya ragu cikin shekaru 10 da suka gabata

2022-10-13 10:48:28 CMG Hausa

Bisa alkaluman da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta bayar a kwanan nan, an ce, matsakacin kudin da suka rage na kashewa na ko wane mutum, bayan an biya haraji ya kai yuan 35128 a shekarar 2021, kwatankwacin dalar Amurka 4940, adadin da ya karu da kaso 112.8 bisa dari idan aka kwatanta da na shekarar 2012. Lamarin da ya nuna cewa, a cikin shekaru 10 da suka gabata, matsakacin saurin karuwar wannan adadi ya kai kaso 8.8 bisa dari a kowace shekara, wanda ya zarce matsakaicin saurin karuwar ma’aunin tattalin arzikin GDPn kasar da kashi 0.5 bisa dari.

Haka kuma, saurin karuwar yawan kudin da suka rage na kashewa na ko wane mutum a yankunan karkarar kasar Sin bayan an biya haraji, ya zarce saurin karuwar adadin a biranen kasar, sakamakon manufofi da matakan kawar da talauci da kokarin raya yankunan karkara da aka gudanar a wuraren, shi ya sa, bambancin yawan kudin shiga tsakanin mazauna birane da na yankunan karkarar kasar Sin na ci gaba da raguwa. Kana, adadin kudin shiga da mazauna yankunan yammaci da tsakiyar kasar Sin yana karuwa cikin sauri, lamarin da ya nuna cewa, bambancin yawan kudin shiga da jama’a suka samu tsakanin yankuna daban daban ya ragu.

Cikin shekaru 10 da suka gabata, yawan kudin shiga da jama’ar kasar Sin suke samu yana ci gaba da karuwa, hakan ya sa, karfin yin sayyaya na jama’ar Sin yake karuwa, lamarin da ya taimaka wajen kyautata zaman rayuwarsu cikin yanayi mai kyau.(Maryam Yang)