logo

HAUSA

Ministoci daga kasashen Afirka 8 sun sha alwashin samar da tsarin wadatar da abinci

2022-10-12 14:39:27 CMG Hausa

Ministoci 8 daga kasashen yankin kahon Afirka, sun sha alwashin samar da wani cikakken tsari na bunkasa samar da isasshen abinci, a gabar da kamfar abinci ke ci gaba da addabar kasashen shiyyar.

Yayin taron ministocin kasashen kungiyar raya yankin ko IGAD, wanda ya gudana a jiya Talata a birnin Nairobi na kasar Kenya, an fitar da sanarwar da ta yi karin haske game da yanayin fari da ake ciki a yankin.

Sanarwar ta ce karancin ruwan sama a damuna 4 a jere cikin shekaru 3 da suka gabata, ya kara ingiza yankuna mafiya fuskantar fari da masu fuskantar matsakaicin fari cikin matsanancin kamfar abinci.

Ministocin kasashen, da jagororin tawagogin kasashe mambobin IGAD dake taron yini biyu, sun ce tsarin da za su samar zai maida hankali ga zakulo matakan dakile fari, da karfafa tsarin samar da abinci, da juriyar kasashen yanki, da fadada cinikayyar albarkatun noma tsakanin kasashen.

Kasashen mambobin IGAD su ne Habasha, da Eritrea, da Djibouti, da Kenya, da Somalia, da Sudan, da Sudan ta kudu, da kuma Uganda.  (Saminu Alhassan)