logo

HAUSA

Ya kamata bai wa yara mata karin damamakin koyon ilmi

2022-10-12 11:09:31 CMG Hausa

Ana bikin ranar yara mata ta duniya ce a ranar 11 ga watan Oktoban kowa ce shekara, domin baiwa yara matan damar bayyana abubuwan dake ci musu tuwo a kwarya. An tsara wannan rana ce da nufin kawar da kalubaloli na bambance-bambancen jinsi da yara matan ke fuskanta a sassa daban-daban na duniya. Kamar auren wuri, inda bayanai ke cewa, kimanin yara mata dubu 33 ake yiwa aure a rana a sassan duniya da tashin hankali da nuna wariya da sauransu.

Taken bikin na bana dai shi ne, “Ranar yara mata:Zamanin Intanet Zamaninmu, Damarmu da ’yancinmu”. Lamarin da ya samar da wata kafa ga al’ummar duniya kara fahimtar matsalolin da wadannan rukuni na al’umma ke fuskanta.

Bayanai na nuna cewa, mutane biliyan 2.2 ’yan kasa da shekaru 25 ba su da hanyar amfani da Intanet, galibinsu yara mata. Tun a ranar 19 ga watan Disamban shekarar 2011 ne, aka fara murnar bikin wannan rana a matsayin ranar yara mata ta duniya. 

Wani kudirin MDD ne ya amince da wannan rana yayin zaman babban zauren MDD, wanda ya ayyana ranar 11 ga watan Oktoba a matsayin ranar yara mata ta kasa da kasa, an kuma nuna cewa, yara maza sun fi takwarorinsu mata samun damammaki a harkoki na rayuwa, kamar ilimi, da aikin yi da makamantansu. Mace daya cikin hudu ba ta da aikin yi, ko rashin samun horo, idan aka kwatanta da namiji daya cikin 10.

Masu fashin baki na cewa, bikin wata da mace ta zakulo kalubalolin da yara mata ke fuskanta a sassan duniya da nufin magance su, ta yadda su ma za su amfana da dukkan damammaki kamar takwarorinsu maza a dukkan fannoni. Mata dai aka ce sune iyayen gida, idan kuma aka ilimantar da mace, tamkar an ilimantar da al’umma ce baki daya. (Samuni, Ibrahim/Sanusi Chen)